Posts

Haaland ba zai buga wasa da Scotland ba saboda raunin da ya ji

Image
  Erling Haaland ba zai buga wa Norway wasan da za ta kara da Scotland ba ranar Lahadi a wasan neman shiga Euro 2024. Dan kwallon Manchester City, mai shekara 23 ya ji rauni a wasan sada zumunta da ƙasarsa ta buga ranar Alhamis da tsibrin Faroe. Tuni dai Scotland da Sifaniya suka samu gurbin buga gasar da za a yi a Jamus a 2024, Norway ce ta uku a cikin rukunin, watakila ta buga wasan cike gurbi. Sai dai hukumar kwallon kafar ta Norway ta ce raunin da Haaland ya ji ba wani mai muni bane.

Super Eagles za ta kara da Zimbabwe ranar Lahadi

Image
    Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya Super Eagles ta sauka a Rwanda a sanyin safiyar Asabar, domin buga wasa da Zimbabwe a neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026. Najeriya za ta buga wasa na biyu a cikin rukuni na uku bayan tashi 1-1 da Lesotho ranar Alhamis. A tsakar daren Asabar Najeriya ta yi shatar jirgin sama daga filin jirgin sama na Victor Attah zuwa Kigali. Daga nan ne za ta shiga motar da za ta yi awa biyu zuwa Butare, inda za ta fafata a filin wasa na Huye, mai cin 'yan kallo 20,000.