Haaland ba zai buga wasa da Scotland ba saboda raunin da ya ji

 

Erling Haaland ba zai buga wa Norway wasan da za ta kara da Scotland ba ranar Lahadi a wasan neman shiga Euro 2024.

Dan kwallon Manchester City, mai shekara 23 ya ji rauni a wasan sada zumunta da ƙasarsa ta buga ranar Alhamis da tsibrin Faroe.

Tuni dai Scotland da Sifaniya suka samu gurbin buga gasar da za a yi a Jamus a 2024, Norway ce ta uku a cikin rukunin, watakila ta buga wasan cike gurbi.

Sai dai hukumar kwallon kafar ta Norway ta ce raunin da Haaland ya ji ba wani mai muni bane.

Comments